Kwamishinan lafiya na jihar Lagas, Jide Idris, ya ce gwamnatin jihar ta kama mutum uku da ke da nasaba da siyar da ganda mai guba a Ojo da kuma Iba.
Jide Idris, ya bayyana hakan ne a ofishinsa a lokacin da yake duba rahoton kwamitin bincike da aka kafa kan Ganda mai guba ya ce an tura mutane uku dake da hannu zuwa kotu, yayinda aka tura samfarin gandar zuwa dakin bincike na hukumar NAFDAC domin gwaji.
Ya ce masu siyar da gandar na aiki a lokuta mabanbanta a wurare daban-daban a kananan hukumomin Ojo da Iba dake jihar.
Daraktan harkokin jama’a na jihar Lagas Adeola Salako ya ce an sami ganda mai guba da yawa daga hannun wadanda aka kama, kuma hukumar na aiki domin tabbatar da lamarin.
Daga karshe an gargadi alummar jihar Legas su guji cin Ganda har sai gwamnati ta kammala tantance Ganadr da aka kama.