Home Labarai Layin Dogo: Gwamnati Za Ta Sake Karbo Bashi Daga Kasar Sin

Layin Dogo: Gwamnati Za Ta Sake Karbo Bashi Daga Kasar Sin

6
0
images 55
images 55

Gwamnati na shirin neman tallafin kudi domin gina layin dogo daga Ibadan zuwa Abuja da Kaduna zuwa Kano.

Ministan sufuri, ne ya bayyana hakan yayin da kwamitin hadin gwiwa na majalisar tarayya kan sufuri ya kai ziyarar duba ayyukan layin dogo na Kaduna zuwa Kano.

Ya ce bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu, ana sa ran mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima zai tattauna da shugaban kasar Sin, Xi Jinping domin samun kudaden.

ya ce rashin kudi ya jawo cikas ga ga cigaban ayyukan layin dogon, yana mai cewa gwamnatin tarayya ta samu rancen kudin kammala titin layin dogon Kano zuwa Kaduna.

Shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin sufurin kasa, Sanata Adamu Aliero ya yi Allah wadai da yadda bata gari ke sace kayan aikin gina titunan.

Sanata Aliero ya ce majalisar za ta tattauna da hukumar kula da basussuka ta kasa (DMO)da  ministan kudi, Antoni Janar na tarayya, da ministan sufuri domin ganin an karbo bashin.

Leave a Reply