Home Labaru Lasisin Bindiga:’Yan Majalisa Sun Bayyana Ra’ayi Kan Umurnin Shugaban Kasa

Lasisin Bindiga:’Yan Majalisa Sun Bayyana Ra’ayi Kan Umurnin Shugaban Kasa

344
0

‘Yan Majalisun dokoki na tarayya sun nuna ra’ayin su kan dokar nan ta shugaban kasa wacce ta soke dukkanin lasisin masu mallakar bindiga a Najeriya.

‘Yan majalisar sun ce kamata ya yi dokar ta soke dukkanin lasisin mallakar kowane irin makami ne a Najeriya ba wai bindiga kadai ba.

Shawarar hakan ta biyo bayan amincewa da kudirin da ‘yar majalisar ta jam’iyyar PDP daga jihar Abia Nnenna Elendu, ta gabatar ne, inda ta ce shugaban kasa ya yi amfani da karfin ikon da yake da shi ne daga sashe na 33 (2) na tsarin mulki kuma wannan dokar ta sabawa sashe na 44 (1) na kundin tsarin mulkin.

Ta ce sashe na 33 (2) ya ce ba za a dauka mutum ya rasa rayuwar sa ba a wajen sabawa wannan sashen, in har ya mutu a sakamakon yin amfani da wannan, a yanayin da doka ta yarje masa, na wannan karfin domin yana zama abin bukata ne domin kare kai.