Home Labaru Lantarki: Kotu Ta Bada Umurni Da A Fallasa ‘Yan Kwangilar Da Su...

Lantarki: Kotu Ta Bada Umurni Da A Fallasa ‘Yan Kwangilar Da Su Ka Ci Kudin Gyara

271
0

Wata babbar kotun tarayya da ke Legas, ta bukaci gwamnatin tarayya ta bayyana sunayen ‘yan kwangilar da su ka ki yin gyaran wutar lantarki bayan sun karbi kudaden aikin.

Mataimakin daraktan kungiyar kare tattalin arzikin kasa da bin diddigi SERAP Kolawole Oluwade, ya ce mai shari’a Chuka Obiazor ne ya bada umurnin a ranar juma’ar da ta gabata.

Ya ce alkalin ya bada umurnin a bayyana cikakken bayani a kan ‘yan kwangilar da aka ba kudin gyaran wutar lantarki tun dawowar dimokaradiyya a shekara ta 1999.

Idan dai ba a manta ba, a cikin watan Fabrairu ne SERAP ta maka tsohon ministan wutar lantarki Babatunde Fashola kotu, inda ta bukaci a umurci Fashola ya bayyana sunayen ‘yan kwangilar da aka ba aikin gyaran wutar lantarki da kuma inda su ke a yanzu, kamar yadda dokar ‘yancin sanin bayanai ta tanada.

A cikin watan Mayu, ministan ya mika wa SERAP sunan wani dan kwangila guda, amma kungiyar ta ce ta na bukatar sunayen sauran ‘yan kwangilar da su ka karbi kudin gyaran wutar amma su ka yi gum ba tare da sun yi aikin ba.

Leave a Reply