Majalisar zartarwa ta kasa ta amince a ranto dala miliyan 247 daga bankin raya nahiyar Afrika da kuma kasar Faransa domin a gyara wutar lantarkin Najeriya.
Ministar kudi ta Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed ta bayyana haka bayan kammala wani taro, inda ta ce daga cikin wannan kudi jihar Legas za ta kashe dala miliyan 20 wajen gyara tituna da kuma gina sabbin hanyoyi.
Ministar ta tabbatar da cewa majalisar ta amince da karbo bashin ne da za a yi amfani da shi wajen inganta wutar lantarkin Najeriya.
Ta ce za’ a kashe wani bangare na kudin wajen kafa na’urorin bada wutar lantarki mai amfani da hasken rana a kauyukan Najeriya, wanda zai taimaka wajen ganin mutane dubu 500 a gidaje fiye da dubu 100 sun samu wutan lantarki.
Ministar ta ce jami’o’i 8 za su amfana, da kuma ‘yan kasuwa fiye da dubu 20 za su ga ribar wannan tsari.
You must log in to post a comment.