Home Labaru Kiwon Lafiya Lafiyar Yara: DFID Ta Tallafa Wa Mata Masu Juna Biyu 52,393 A...

Lafiyar Yara: DFID Ta Tallafa Wa Mata Masu Juna Biyu 52,393 A Jihar Zamfara

619
0

Shirin inganta kiwon lafiyar kanana yara CDGP, da ke karkashin kungiyar ci-gaban tarayyar Turai, ya tallafa wa mata masu dauke da juna biyu har dubu 52 da 393 a jihar Zamfara.

Jami’in shirin Tanko Muhammed ya bayyana haka, a wajen taron tattauna hanyoyin tallafa wa mutanen karkara da shirin ke yi a garin Gusau.

Mohammed, ya ce shirin ya tallafa wa mata masu juna biyu a kauyuka 527 da ke kananan hukumomin Anka da Tsafe da Naira 4000 duk wata, domin kula da ‘ya su tun daga shekara ta 2014 zuwa 2019.

Ya ce an fara gudanar da shirin ne a shekara ta 2014, domin inganta kiwon lafiyar kananan yara a jihohin Jigawa da Zamfara, inda ake ba kowace mace naira 4000 a kowane wata domin kula da kan ta. Mohammed ya yaba wa goyan bayan da su ke samu daga shugabannin kananan hukumomin Tsafe da Anka wajen ganin shirin ya yi nasara.

Leave a Reply