Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai samar da ingantattun magunguna cikin rahusa a Nijeriya.
Shugaban Kamfanin hada magunguna na Graham Foggs ya bayyana haka a lokacin da ya ke ganawa da manyan kamfanonin hada magunguna na kasar Sin.
Tawagar kamfanin ta je kasar sin ne domin kulla yarjejeniyar kasuwanci da kamfanonin hada magungunan domin samar da ingantattun magunguna a Nijeriya.
Daga cikin manufar kulla jarjejeniyar a kwai samar da kayayyakin hada magunguna a duk inda suke a duniya, da kuma hada magunguna a Nijeriya wanda hakan zai saukaka wajen samun magunguna masu saukin farashi mai sauki .
You must log in to post a comment.