Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kwazon Aiki: Shugaba Buhari Ya Yi Wa Wasu Hafsoshin Soji Karin Girma

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi wa wasu manyan hafsoshin sojin Nijeriya karin girma, sakamakon gagarumar rawar da su ka taka wajen aikin samar da tsaro.

A cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na ma’aikatar tsaro ta Nijeriya Kanar Sagir Musa ya sanya wa hannu, ta ce an kara wa Manjo Janar Lamidi Adeosun girma daga mukamin sa na yanzu zuwa Laftanar Janar, yayin da aka kara wa kwamandan runduna ta 7 Birgediya Janar Abdulmalik Bulama Biu girma zuwa mukamin Manjo Janar.

Kanal Sagir Musa, Daraktan yada labarai na ma’aikatar rundunar soji ta Nijeriya

Sanarwar ta cigaba da cewa, an kuma kara wa Laftanar AJ Danjibrin girma zuwa mukamin Kyaftin.

Shugaban rundunar dakarun sojin kasa ta Nijeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, ya taya hafsohin murna dangane da wannan karin girma da su ka samu.

Exit mobile version