Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara wa shugaban alkalan Nijeriya Tanko Muhammed wa’adin watanni uku a kan kujerar sa da ke rikon kwarya.
Mai Magana da hukumar kula da ma’aikatar shari’a ta kasa NJC Soji Oye, ya ce shugaba Buhari ya aika takardar neman karin wa’adin ga hukumar.
Idan dai ba a manta ba, a watan Janeru ne shugaba Buhari ya nada Tanko Muhammad a matsayin shugaban alkalai na kasa, bayan dakatar da tsohon shugaban alkalai Walter Onnoghen wanda ake zargi da kin bayyana dukkanin kaddarorin da ya mallaka. A ranar Alhmis din da ta gaba ne, kotun da’ar ma’aikata ta kasa ta tabbatar da samun Walter Onnoghen da laifin zargin sa da kin bayyana kaddarorin sa da ya mallaka da gangan, wanda daga karshe kotun ta haram ta mashi rike dukkanin wani mukami har na da tsawon shekaru 10.