Jami’ar Bayero da ke Kano, za ta karrama shararren masanin harkar masanantu da hada-hadar kudade kuma shugaban rukunin Bankin UBA Tony Onyemaechi Elumelu, da babbar Lauya mace ta farko Folake Solanke, da Sanata Bello Hayatu Gwarzo da digirin girmamawa, bisa gudunmuwar da su ke badawa ta fuskar inganta rayuwar al’umma.
Za a karrama shahararrun mutanen ne a wajen bikin yaye dalibai karo na 35 da jami’ar za ta yi a ranar 15 ga watan Yuni na Shekara ta 2019.
Haka kuma, jami’ar za ta yi wa Farfesa Abdulkadir Dambo, wanda ya yi marabus daga aiki bayan gudunmuwar da ya ba jami’ar tsawon shekaru 37 da kuma gudunmuwar da ya ke ci-gaba da badawa, karramawa ta musamman kamar yadda shugaban jami’ar ya bayyana.
Shugaban jami’ar ya ce an zabi a karrama mutanen ne bisa cancanta bayan dogon nazari.