Home Labarai Kwastam Ta Kama Tsundukai Ɗauke Da Tulin Makamai A Ribas

Kwastam Ta Kama Tsundukai Ɗauke Da Tulin Makamai A Ribas

93
0
17ea5990 37b4 11ef bdc5 41d7421c2adf.jpg
17ea5990 37b4 11ef bdc5 41d7421c2adf.jpg

kwastam ta sanar da kama manyan kwantenoni guda makare da makamai da muggan kwayoyi da aka ɗauko su daga kasar Turkiyya.

Shugaban hukumar ne ya bayyana hakan yayin da yake yiwa manema labarai karin bayani a gaɓar ruwan Onni da ke Fatakwal.

Mista Adewale ya ce darajar kayayyakin da aka kama ta kai naira biliyan 13 da miliyan 900.

Shugaban ya kuma ƙara da cewa abin mamakin shine yadda masu laifin suka yi nasarar fitowa da kayan daga kasar Turkiyya suka kuma iso da su Najeriya ba tare da an iya kama su ba, la’akari da yawan kayan.

Yayin da yake bayani, ya yabawa jami’an hukumar da kuma wasu jami’an sirri da ke aiki a gaɓar ruwan, yana mai cewa da wannan bayani ne aka yi amfani wajen kama kayan.

Bayanai sun nuna cewa darajar kudin fiton kayan kadai ya zarta Naira biliyan 4 da miliyan 200, kuma tuni aka kama mutane uku da ke da hannu a safarar kayayyakin.

Leave a Reply