Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kwanton Bauna: Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Boko Haram A Yobe

Sojojin Najeriya sun yi nasarar hallaka mayakan Boko Haram da dama, a wani kwantan bauna da dakarun suka yi musu a jihar Yobe a yammacin ranar Talata.

A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ta ce rundunar su ta yi wannan nasara ne sakamakon bayanan da suka samu a kan yunkurin mayakan Boko Haram na kai hari Damaturu, babban birnin jihar ta Yobe.

Sanarwar ta kara da cewa, dakarun Najeriya masu yaki da Boko Haram sun samu nasarar yi wa mayakan Boko Haram din kwanton bauna ne inda suka hallaka da dama daga cikin su.

Dakarun sun yi kwanton bauna ne a wani wuri da ba shi da nisa daga garin Mai Sandari, wanda ke wajen babban birnin jihar ta Yobe wato Damaturu.

Sanarwar ta ce, dakarun sun ci karfin masu tayar da kayar bayan ne, saboda irin makaman da suke da su da kuma taimakon jiragen yakin su.

Baya ga wadanda aka kashe, akwai wasu ‘yan Boko Haram da suka samu raunuka a artabun.

Dakarun sun kuma ce sun yi nasarar kwace makamai masu yawa daga ‘yan Boko Haram.

Exit mobile version