Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta ce a lokacin Sanata Stella Oduah ta kan kujerar Minista, ta karkatar wasu daga cikin Naira biliyan 9 da rabi da aka ware domin sayen kayan tsaro a filayen sauka da tashin jiragen sama na Nijeriya.
EFCC, ta ce Stella Oduah ta wawuri kudaden ne a lokacin da ta ke rike da Ministar harkokin jirgin sama na Nijeriya.
Hukumar EFCC ta gabatar da bayanin ne a cikin hujjojin ta na maka tsohuwar Ministar kotu.
Yanzu haka dai EFCC ta samu nasarar karbe kayan da Sanatar ta saya da kudin da ake zargin ta sata daga asusun gwamnati, biyo bayan umurnin da alkalink Kotun ya bada.
Tsakanin shekara ta 2012 zuwa 2014, ake zargin ministar ta hada baki da bankuna wajen yin awon-gaba da kudin da ta bada na sayen kayan sa-ido a filayen jirgin sama.