Home Labaru Kwallon Kafa: Obi Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ya Kaurace Wa...

Kwallon Kafa: Obi Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ya Kaurace Wa Super Eagles

505
0

Kaptin na ‘yan was an kwallon kafa ta Nijeriya Super Eagles John Mikel Obi, ya ce shawarar kaurace wa tawagar da ya yi ba ta da nasaba da abin da ya faru a gasar cin kofin duniya ta shekara ta 2018 a kasar Rasha.

Mikel dai bai fafata a ko daya daga cikin wasannin cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ba, amma ya zo don a dama da shi a gasar, wadda za a fara a Masar ranar 21 ga watan Yuni.

Tsohon dan wasan na Chelsea, ya ce shawarar sa ba ta da nasaba da rashin nasarar da Najeriya ta yi tun daga matakin rukuni.

Ya ce bayan ya tattauna da kocin tawagar ne ya yanke shawarar janyewa daga tawagar, duba da cewa ya shafe shekaru 15 ya na buga mata wasa, tun daga lokacin da ya fafata a gasar cin kofin duniya ta matasa ‘yan kasa da shekaru 17 da aka yi a kasar Finland a shekara ta 2003.

Leave a Reply