Home Labaru Kwallon Kafa: Musa Da Iwobi Da Abdullahi Sun Isa Sansanin Super Eagles

Kwallon Kafa: Musa Da Iwobi Da Abdullahi Sun Isa Sansanin Super Eagles

620
0

Manyan ‘yan wasan tawagar kwallon kafa ta Nijeriya, da su ka hada da Ahmed Musa, da Alex Iwobi da Shehu Abdullahi, sun isa sansanin tawagar Super Eagles a Otal din Golden Tulip da ke Asaba ta jihar Delta.

Da maraicen ranar Larabar da ta gabata ne ‘yan wasa uku su ka sauka, wanda hakan ya kai jimillar ‘yan wasan da ke sansanin zuwa 23, kuma ana sa ran dan wasan baya na Udinese, William Troost Ekong ya sauka a kowane lokaci daga yanzu.

A ranar Asabar mai zuwa ne, tawagar Super Eagles za ta barje gumin ta a wasan sada zumunta da kasar Zimbabwe, a filin wasa na Stephen Keshi da ke Asaba, duk a cikin shirin tunkarar gasar cin kofin nahiyar Afirka ta shekara ta 2019 da za ta gudana a Masar.

Bayan wasan, ana sa ran kocin tawagar kwallon kafa ta Nijeriyan Gernot Rohr ya bayyana sunayen ‘yan wasa 23 da za su wakilci Nijeriya a gasar ta nahiyar Afirka.

Tawagar za ta bar Nijeriya zuwa kasar Masar a ranar Lahadi mai zuwa, domin ci-gaba da shirye-shiryen yin gumurzu a gasar, inda za ta hadu da Burundi, da Guinea da kuma Madagascar a rukunin B.

Leave a Reply