Home Labaru Kwallon Kafa: Arsenal Za Ta Bada ‘Yan Wasa Uku Da Kudi Don...

Kwallon Kafa: Arsenal Za Ta Bada ‘Yan Wasa Uku Da Kudi Don Daukar Dan Wasan Afrika

1069
0

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da ke kasar Ingila, ta nuna sha’awar bada ‘yan wasan ta uku da kuma karin kudi domin daukar dan wasan gaba na kungiyar Crystal Palace, kuma dan asalin kasar Ivory Coast da ke nahiyar Afrika Wilfred Zaha.

Zaha, mai shekaru 26, ya samu nasarar jefa kwallo 10 a wasanni 36 da ya buga wa kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace a kakar wasannin bana.

A karshen watan da ya gabata ne, Zaha ya sanar da cewa ya na da sha’awar taka leda a gasar wasannin cin kofin zakarun nahiyar Turai UCL a kakar wasanni ta shekara mai zuwa, lamarin da ya tilasta Crystal Palace barin dan wasan ya tashi daga kungiyar.

An dai yi kiyasin cewa, darajar Zaha ta na tsakanin Yuro miliyan 65 zuwa 80, adadin kudin da ya yi daidai da tanadin da kungiyar Arsenal ta yi domin sayen dan wasan gaba idan ta samu nasarar zuwa gasar cin kofin UCL a kakar wasanni ta badi.

Arsenal dai na fatan zuwa gasar UCL a kakar wasanni ta badi, idan ta samu nasarar doke kungiyar Chelsea a wasan karshe da za su buga a gasar cin kofin nahiyar Turai UEFA a ranar Laraba mai zuwa.