Home Labaru Kwallon: Barcelona Ta Kara Nisa A Saman Teburi

Kwallon: Barcelona Ta Kara Nisa A Saman Teburi

908
0

Barcelona ta bayar da tazarar maki 11 a saman teburi bayan ci 2-0 da ta yi wa Athletico Madrid a zazzafan wasan hamayya da suka buga.
Luis Suarez da Lionel Messi ne suka ci wa Barce kwallaye masu kyan gaske, wanda ya kara dora su a hanyar lashe kofin La Liga na biyar cikin shekaru bakwai.
Tun kafin a tafi hutun rabin lokaci aka, kori tsohon dan wasan Chelsea Diago Costa bayan ya ci mutuncin alkalin wasa Jesus Gil a minti na 27.
Suarez ne ya fara jefa kwallo ana saura minti biyar a tashi daga wasan, inda Messi ya ci kwallo ta biyu dakika 60 bayan haka a minti na 86.

Leave a Reply