Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kungiyoyin Kasashen Waje Ne Ke Daukar Nauyin Boko Haram – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce wasu kungiyoyin kasa da kasa ne ke daukar nauyin ayyukan Boko Haram a Nijeriya.

Buhari ya bayyana haka ne, yayin wata liyafar cin abincin shugaban kasa da gwamnatin Jihar Kano ta shirya masa a ziyarar aikin wu daya da ya kai.

 Ya ce lokacin da su ka hau mulki a shekara ta 2015, Boko Haram sun mamaye kananan hukumomi 13 daga cikin 17 na Jihar Borno.

Buhari ya kara da cewa, dole ne a dage da addu’a, kuma za su yi yakin kwato kasar nan daga kungiyoyin kasa da kasa da ke kokarin ruguza Nijeriya. Tun farko dai Gwamna Abdullahi Ganduje ya yaba wa shugaba Buhari bisa yadda ya ke martaba Jihar Kano.

Exit mobile version