Home Labarai Kungiyar NUPENG Ta Yi Wa Ƙungiyar Ƙwadago Mubaya’ar Shiga Zanga-Zanga

Kungiyar NUPENG Ta Yi Wa Ƙungiyar Ƙwadago Mubaya’ar Shiga Zanga-Zanga

22
0

Ƙungiyar Gamayyar Ma’aikatan Harkokin Man Fetur da Gas NUPENG, ta bayyana goyon bayan cewa za ta shiga cikin zanga-zangar da Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa NLC za ta yi a kan yajin aikin da malaman jami’o’i ke yi a ƙarƙashin ASUU.

Tun farko dai Shugaban kungiyar Kwadago ta kasa Ayuba Wabba, ya ce Ƙungiyar za ta fito zanga-zanga idan yajin aikin ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

An dai shafe tsawon watanni biyar malaman jami’o’i su na yajin aiki, wanda su ka fara tun a ranar 14 Ga Fabrairu.

A cikin wata sanarwa da kungiyar NUPENG ta fitar, ta soki lamirin gwamnatin tarayya, saboda ta kasa magancewa da kuma shawo kan yadda za a daina yajin aikin.

Ta ce za su shiga zanga-zanga domin taya NLC nuna wa gwamnati damuwar su a kan mawuyacin halin da jami’o’in Nijeriya ke ciki.