Kungiyar matasa ta Arewa Youth for peace and security ta bukaci shugaban kasa da ya sanya baki wajen biyan ma’aikatan majalisar kula da magunguna ta kasa wato Pharmaceutical Concil of Nigeria saboda rashin kasafin kudin su na shekara ta 2024.
A cikin wata sanarwar manema labarai da Sakataren kungiyar Comared Salihu Mahmud ya sanya wa hannu.
ya bayyana cewar majalisar ta PCN na taka rawar ganin wajen inganta lafiyar jama’a da dakile hada- hadar magungunar Jabu bai kama ace suna aiki hannu rabbana ba.
Sanarwar ta kara da cewar PCN ta gabatar da kasafin kudinta na 2024 ga ofishin kasafi na kasa inda aka ce mata ta jira har sai lokacin ya yi, daga bisani kuma ta yi batan bakatantan.
Majalisar ta roki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umurnin fitar da kudi domin samar musu da mafita wajen biyan albashin su,
Don kula da iyalan su kada su fada cikin karbar cin hanci da rashawa wanda hakan mummunar dabi’a ce ga cigaban kasa.