Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kungiyar IPMAN Ta Yi Karin Haske A Kan Yiwuwar Litar Man Fetur Ya Koma N700

Kungiyar dilllan man fetur IPMAN, ta yi watsi da jita-jitar da
ke yawo a kan batun karin kudin litar man fetur da kusan
Naira 500, inda ta ba mutane shawarar su daina sayen fetur su
boye saboda tsoron tashin farashi.

Shugaban kungiyar na yankin Kudu maso yamma Alhaji Dele Tajudeen ya bayyana haka a garin Ibadan na jihar Oyo ya na mai musanta rade-radin.

Dele Tajudeen, ya ce sun karanta labarai a jarida cewa wani ya na maganar fetur zai kara tsada, ya na mai cewa hasashe ne kawai wanda ba gaskiya ba.

Dan kasuwan ya tabbatar wa talaka cewa, tashin Dalar Amurka zuwa Naira 700 ko 800 ba zai janyo farashin fetur ya tashi daga Naira 500 zuwa Naira 700 ba.

Exit mobile version