Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kungiyar CNG Ya Bukaci EFCC Ta Hana Duk Na Kusa Da Buhari Barin Nijeriya

Gamayyar Kungiyoyin Arewa CNG, ta bukaci hukumomin
yaki da cin hanci da rashawa cewa kada su bar wadanda su ka
rike mukami a gwamnatin shugaba Buhari su bar Nijeriya.

Kungiyar dai ta na magana ne, a kan wadanda ake zargi da cin hanci da rashawa a gwamantin da ta ta gabata, musamman gwamnan babban bankin Nijeriya Godswill Emefiele bisa zargin da ake yi masa.

Mai Magana da yawun Kungiyar Abdul-Azeez Suleiman ya bayyana haka yayin wani taro da su ka gudanar, inda kungiyar ta soki masu neman kawo cikas a rantsarwar da aka gudanar a Abuja.

Kungiyar, ta kuma bukaci Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta kara bincike a kan badakalar da ake yi a ma’aikatu da sauran hukumomin gwamnati domin gurfanar da masu laifi.

Exit mobile version