Home Labaru Kuncin Rayuwa: Sultan Ya Ce Dole Gwamnati Ta Kauda Kalubalan Da Ake...

Kuncin Rayuwa: Sultan Ya Ce Dole Gwamnati Ta Kauda Kalubalan Da Ake Fuskanta A Nijeriya

587
0

Sarkin Musulmi Alhaji Abubakar Sa’ad na uku, ya bayyana damuwar sa a kan yadda rashin tsaro da matsin rayuwa su ka yi wa Nijeriya katutu.

Ya ce gwamnatin Nijeriya ba ta da wani uzuri na rashin kawo karshen kalubalen da ake fuskanta a Nijeriya, musammam a kan yadda rashin tsaro da talauci da kuncin rayuwa su ka yi wa kasar nan sarkakiya.

Sarkin Musulmi, ya ce akwai babbar damuwa game da yadda aka gaza warware matsalolin da Nijeriya ke fuskanta a halin yanzu.

Sultan ya bayyana haka ne, a wajen taron shekara na kungiyar Jama’atu kamar yadda aka saba domin yi wa watan Azumin Ramalana maraba da ya gudana a Kaduna.

Ya ce duk da arzikin jagorori nagari da kuma macancanta, Nijeriya ba ta da wani uzuri na gazawar ta a kan rashin warware matsalolin da al’ummar kasar nan ke fuskanta a halin yanzu.

Leave a Reply