Gwamnatin tarayya ta yi zargin cewa, wasu jihohin 14 sun ki shiga cikin shirin kula da lafiyar da zai ba su damar amfana da kudaden da aka ware domin kula da lafiyar al’ummar su.
Ministan Lafiya Isaac Adewole ya shaidawa majalisar dattawa cewa, yanzu haka jihohi 22 ne suka yi rajistar cin gajiyar shirin, kuma tuni aka sakar masu kudaden kai tsaye zuwa cibiyoyin kula da lafiya a matakai daban daban da ke jihohin su.
Adewole ya kara da cewa, jihohin da suka ki shiga shirin sun hada da Kebbi da Jigawa da Akwa Ibom da Cross Rivers da Borno da kuma Zamfara da Ondo da Benue da Taraba da Nasarawa da Ogun da kuma Sokoto.
Sharudodin cin gajiyar shirin sun hada da kafa hukumar kula da lafiya a matakin farko, da kaddamar da shirin inshoran lafiya na jiha, sai kuma bada wani kashi na kudaden da za’a zuba wajen kula da lafiya al’umma.