Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin tarayya na shirin fadada shirin inshoran lafiya na kasa domin kula da lafiyan ‘yan Najeriya.
Mataimakin shugaban kasa ya yi wannnan jawabin ne a wurin taron kaddamar da tsarin inshoran lafiya na jihar Bauchi, inda ya ce za a fadada shirin hukumar a cikin mataki na gaba domin tabbatar da cewar ‘yan Najeriya sun samu kulawa ta fannin lafiya.
Ya ce akwai bukatar dukkan gwamnatocin jihohi su kafa na su shirin samar da inshoran lafiya domin tallafawa na gwamnatin tarayya wurin samar da ingantataccen kulawa ga lafiya.
Osinbajo ya ce jihar Bauchi ita ce tafi amfana da shirin gwamnatin tarayya na tallafawa ‘yan kasa da rage radadin talauci, saboda matasa 14,075 na jihar Bauchi sun amfana da shirin N-Power yayin da daliban makarantun firimare 618,214 ne ake ciyarwa a kullum karkashin shirin ciyar da daliban makaranta. A kalla manoma 9,799 sun samu bashi mai saukin biya karkashin shirin Micro-Credit, su kuma ‘yan kasuwa 29,000 sun samu tallafi karkashin shirin Trader-Moni, a yayin da masu karamin karfi 23,000 na amfana da tallafin gwamnati.