Home Labaru Kiwon Lafiya Kula Da Lafiya: Cutar Kyanda Ta Hallaka Yara 1,500 A Kasar Congo

Kula Da Lafiya: Cutar Kyanda Ta Hallaka Yara 1,500 A Kasar Congo

460
0

Jami’an lafiya a Jamhuriyar Congo sun yi shelar barkewar annobar cutar kyanda a fadin kasar, wadda bincike ya nuna cewa annobar ta hallaka mutane dubu 1, da 500.
Yayin da yake kari bayani kan halin da ake ciki, dangane da barkewar annobar, ministan lafiya na Jamhuriyar ta Congo, Oly Ilunga Kalenga, ya ce daga farkon shekarar 2019 da muke ciki zuwa yanzu, an yara akalla dubu 87 ne suka kamu da cutar Kyandar.
Ministan ya kuma kara da cewa annobar kyandar ta shafi larduna 23 daga cikin 26 da ke fadin kasar, saboda haka ya zama tilas a sake kaddamar da shirin rigakafin kamuwa da cutar.
A watan Afrilu da ya gabata, kananan yara miliyan 2 da kusan rabi ka yiwa ragakafin cutar kyanda a Jamhuriyar Congo, masu watanni 6 zuwa shekara guda a duniya, nan da kwanaki kalilan domin yiwa Karin yara miliyan 1 da dubu 400 rigakafi.
A watan Agustan shekarar bara, ma’aikatar lafiyar kasar ta ce annobar cutar kyandar data barke tayi sanadin halaka kananan yara dubu 1, da 384.

Leave a Reply