Home Labaru Kiwon Lafiya Kula Da Lafiya: Buhari Ya Kaddamar Da Sabon Asibitin Sojojin Sama A...

Kula Da Lafiya: Buhari Ya Kaddamar Da Sabon Asibitin Sojojin Sama A Daura Da Ke Katsina

838
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da asibitin dakarun sojojin sama na Najeriya a garin Daura dake Jihar Katsina.

Shugaban kasa Buhari ya bayar da tabbacin zai yi duk mai yi wu wa domin ganin an samar da dukkannin kayayyakin aikin da ake bukata a asibitin ‘yan Najeriya za su samu ikon amfana da shi.

Ya ce a shekaru hudu da suka gabata, gwamnatin sa ta ware kudade masu yawa a fannin kiwon lafiya ta hanyar kara adadin da ake warewa fanin a kasafin kudin kasa daga naira biliyan 259 a shekara ta 2015 zuwa naira biliyan 340 a shekara ta 2018.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bude asibitin dakarun sojojin sama

Wasu daga cikin manyan mutanen da suka samu hallartan taron kaddamar da asibitin sun hada da gwamna Bello Muhammad Matawalle na Zamfara da gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje da gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina da shugaban hafsin sojojin sama, Sadique Abubakar.

Leave a Reply