Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kula Da Ilimi: Gwamnan Zamfara Ya Amince A Maida Da Malamai 556 Da Gwamnatin Yari Ta Kora

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya amince a maido da malaman makaranta 556 da gwamnatin da ta shude ta kora.

Hakan dai, na kunshe ne a cikin takardar da babban daraktan yada labarai na jihar Yusuf Idris ya sa wa hannu, kuma ya aika da ita ga manema labarai a birnin Gusau.

Yusuf Idris ya ce, tuni gwamnan ya umarci shugaban ma’aikatan jihar da a fara biyan albashin ma’aikatan a watan Satumba.

Matawalle, ya jinjinawa malaman a kan hakurin su da juriya, sannan ya  hore su da su kasance masu dabi’a ta kwarai a yayin da suka dawo nakin aikin su.

Gwamnan ya kara da cewa, dawo da su aiki na daya daga cikin kudirin gwamnatin sa na sauraro da kuma share kukan masu koke.

Idan dai ba a manta ba, a cikin makon da ya gabata ne malaman suka kai koken su ga gwamna Matawalle, inda nan take ya umarci shugaban ma’aikatan jihar Kabiru Balarabe da ya tantance ingancin koken tare da fitar da ingantaccen rahoto a kan haka.

Bayan gudanar da binciken ne dai, shugaban ma’aikatan ya ce akwai inganci a maganganun su, sai gwamnan ya amince da dawo da su bakin aikin su.

Exit mobile version