Dan Gwamnan Jihar Kano Abba Ganduje, wanda ya tsaya
takarar dan Majalisar Wakilai a karkashin jam’iyyar APC ya
ce bai yarda da sakamakon zaben da ya ba jam’iyyar NNPP
nasara ba.
Hukumar Zabe ta Kasa dai ta ayyana Injiniya Tijjani Abdulkadir Jobe a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Dawakin Tofa da Rimin Gado a karkashin jam’iyyar NNPP.
Tuni dai Umar, wanda aka fi sani da Abba Ganduje ya maka Tijjani Jobe a gaban kotun sauraren kararrakin zabe.
Ta bakin lauyan sa Barista A.T Falola, Abba Ganduje ya kuma kalubalanci hukumar zabe a kan ayyana Jobe a matsayin dan takarar da ya samu rinjayen kuri’un da aka jefa a lokacin zabe.
Da ya ke gabatar da kara a gaban kotun, Falola ya roki kotun ta gudanar da shari’ar a kan Jobe da kuma jam’iyar sa ta NNPP.