Home Labaru Kudiri: Shugaba Buhari Ya Ce Zai Ba ‘Yan Nijeriya Mamaki A Wa’adin...

Kudiri: Shugaba Buhari Ya Ce Zai Ba ‘Yan Nijeriya Mamaki A Wa’adin Mulkin Shin A Biyu

330
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sha alwashin ba wadanda ke kiran sa da sunan ‘Baba Go Slow’ mamaki a wa’adin mulkin sa na biyu.

Buhari ya bayyana haka ne, lokacin da yake zantawa da manema labarai ta kafar talabijin na Nijeriya NTA.

Bayan soma wa’adin mulkin sa na farko, shugaban Buhari ya fuskanci suka daga bangarori daban-daban game da yadda gwamnatin sa ke jan-kafa wajen aiwatar da wasu mahimman al’amurra.

Sai dai yayin da ya ke shan alwashin ba ‘yan Nijeriya mamaki a zangon shugabancin sa na biyu, Buhari ya yi alkawarin tabbatar da ganin an yi wa rundunar ‘yan sanda da sashen shari’a garambawul.

Dangane da yawaitar ayyukan ta’addanci kuwa, Buhari ya dora kaso mafi tsoka na alhakin tabarbarewar tsaro a kan jami’an ‘yan sanda da shugabannin al’umma a unguwanni da kuma kauyuka.