Home Labaru Kudin Shiga: FAAC Ta Raba Wa Gwamnatoci Naira Biliyan 679.69 Na Watan...

Kudin Shiga: FAAC Ta Raba Wa Gwamnatoci Naira Biliyan 679.69 Na Watan Mayu

481
0

Kwamitin rarraba kudaden gwamnatin tarayya FAAC a takaice, ya kasafata wa gwamnatocin tarayya da jihohi da kananan hukumomi naira biliyan 679 da miliyan 69 na watan Mayu.

Daraktan yada labarai na ma’aikatar kudi Hassan Dodo ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Kano, inda ya bayyana adadin yawa kudaden da kowace jiha da gwamnatin tarayya da kananan hukmomi su ka samu.

Ya ce gwamnatin tarayya ta samu naira biliyan 284 da miliyan 16, yayin da jihohi su ka samu naira biliyan 187 da miliyan 6, kakanan hukumomi kuma sun samu naira biliyan 140 da miliyan 99.

Hassan Dodo ya kara da cewa, jihohi masu albarkatun man fetur kuma sun samu kusan naira biliyan 40 da miliyan 43, wanda ya yi daidai da kashi 13 cikin 100 na kudaden da ake raba wa gwamnatocin kamar yadda aka saba a kowane wata.

Leave a Reply