Home Labaru Kasuwanci Kudin Shiga: Buhari Ya Zartar Da Hukuncin Karshe A Kan Kadarorin Da...

Kudin Shiga: Buhari Ya Zartar Da Hukuncin Karshe A Kan Kadarorin Da Aka Kwato

706
0
Zainab Ahmed, Ministar Kudi
Zainab Ahmed, Ministar Kudi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ba ministar kudi Zainab Ahmed umarnin a saida duk kadarorin da aka kwace daga hannun mutanen da ake tuhuma da laifuffukan cin hanci a cikin watanni shida.

Wannan hukunci dai zai shafi ‘yan siyasa da dama, wadanda su ka hada da tsofaffin gwamnoni da ma’aikatan gwamnati a matakai daban-daban.

Ministan kasafi Udoma Udo Udoma, ya ce gwamnatin tarayya ta kammala shirin bunkasa hanyoyin samun kudin shiga a shekara ta 2019.

Udo Udoma, ya ce yanzu haka ma’aikatar kudi ta fara aiki da hukumomin da ke da ruwa da tsaki domin fara saida kadarorin kamar yadda shugaba Buhari ya bada umarni.Ya ce shugaba Buhari ya ba sashen kula da farashin man fetur umurnin tattara lasisi da takardun harajin ‘yan kasuwar man fetur tun daga shejara ta 2017 domin a gano wadanda ake bi bashi, yayin da aka ba kamfanin NNPC umarnin tabbatar da an saida gangar man fetur miliyan 2 da dubu 300 a kowace rana, kamar yadda ya ke a cikin jadawalin su na wannan shekarar.

Leave a Reply