Tsohon sakataren jam’iyyar PDP na kasa Olisah Metuh ya bayyanawa babbar kotun tarayya da ke Abuja yadda ya rabar da miliyan dari hudu da ya karba a wajen tsohon mai ba shugaban kasa shawara a harkokin tsaro Sambo Dasuki.
Idan dai ba a manta ba, hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC na tuhumar Olisah Metuh da kamfanin sa mai suna Destra Investment da laifin fitar da kudi har naira miliyan dari hudu ta hanyar da bata dace ba.
Metuh ya ce akwai kudi kimanin naira miliyan 7 da dubu dari 5 da aka biya kamfanin CNC a ranar 2 ga watan Disamba, da kuma naira miliyan 21 da dubu 7 da aka turawa Cif Anenih, sannan kuma da naira miliyan 50 da aka tura a ranar 4 ga watan Disambar shekara ta 2014.
Duk a ranar dai, an turawa Richard Ehidioha naira miliyan 31 da dubu dari 5, sannan kuma ya sa ke sanar da kotu yadda aka biya kamfanin Daniel Ford International naira miliyan 200 da kuma miliyan 300 duka a ranar 4 ga watan Disambar.
Yanzu haka dai, alkalin kotun ya daga sauraron karar zuwa ranar 30 ga watan Satumbar 2019, domin cigaba da sauraron shari’ar.
You must log in to post a comment.