Home Labarai Kudin Fansa: Shugaba Tinubu Ya Ce Ba Zai Biya Ƴanbindiga Ko Sisin...

Kudin Fansa: Shugaba Tinubu Ya Ce Ba Zai Biya Ƴanbindiga Ko Sisin Kwabo Ba

163
0

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya umarci jami’an tsaro kada su kuskura su biya kuɗin fansar sakin kusan ɗalibai 300 da malamin su da aka yi garkuwa da su makon da ya gabata daga wata makaranta da ke Kuriga yankin karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

Ministan yaɗa labarai, Muhammed Idris ya shaida wa manema labarai cewa Shugaban kasan ya kuma umarci hukumomin tsaron su tabbatar an kuɓutar da dukkan mutanen da aka sace ba tare da biyan ƴan bindigar kuɗin fansa ba.

Tun farko dai ƴan’uwan ɗaliban sun ce ƴanbindiga sun buƙaci a biya su kuɗi mai yawa domin su saki yaran da suka sace daga makarantar su a ƙauyen Kuriga.

Cikin makon da ya gabata, an sace mutane da dama ciki har da fiye da mutum 60 na baya-bayan nan a garin Buda dake karamar hukumar Kajuru jihar ta Kaduna.

Leave a Reply