Home Labaru Kudaden Lamuni: Gwamnati Za Ta Dawo Da Bashin Naira Biliyan 614 Da...

Kudaden Lamuni: Gwamnati Za Ta Dawo Da Bashin Naira Biliyan 614 Da Ta Ba Jihohi 35

324
0
Zainab Ahmed, Ministar Kudi
Zainab Ahmed, Ministar Kudi

Gwamnatin tarayya ta fara wani shirin tattaro kudaden lamunin da ta ba jihohi 35 ban da jihar Legas bashi wanda yawan su ya kai Naira miliyan dubu 614.

Ministar kudi da kasafi da tsare-tsare Zainab Ahmad, ta ce tuni taron kolin tattalin arziki da ya gudana a ranar alhamis karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ya amince da kafa wata tawaga daga kungiyar gwamnoni da zata gana da babban bankin Najeriya don fara daukar matakin dawo da kudaden.

Rahotanni sun bayyana cewa kowacce jiha cikin jihohin 35 ta karbi kudin da yawan su ya kai Naira miliyan dubu 17 da doriya sai dai banda jihar Lagos.