Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya ba al’ummar Jihar Katsina haƙuri dangane da mawuyacin halin da ‘yan jihar da ma ƙasa baki ɗaya su ka shiga sakamakon canjin kuɗi da Babban Bankin Nijeriya ya yi.
Buhari ya bayyana haka ne, yayin wani jawabi da ya yi wa al’ummar jihar Katsina a gidan sa da ke garin Daura, inda ya yi godiya a kan yadda aka zaɓe shi har sau biyu a matsayin shugaban ƙasa karkashin jam’iyyar APC.
Shugaba Buhari, ya ce ya na ba jama’a haƙuri bisa wahalar da aka sha ta canjin kuɗi, sai dai ya ce an yi haka ne domin haɓɓaka tattalin arziki.
Haka kuma, Buhari ya roƙi al’ummar jihar Katsina su zabi ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC Dikko Umar Raɗɗa da ‘yan majalisar jiha na jam’iyyar.