Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci dakarun sojin Nijeriya su ci-gaba da fatattakar ‘yan ta’adda a yankin tafkin Chadi da kuma yankin Arewa maso gabashin Nijeriya.
Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke ganawa da gwamna jihar yobe Mai Mala Buni a fadar sa da ke Abuja, inda ya kara da cewa akwai bukatar jami’an tsaron Nijeriya su ci gaba da kokari domin kawo karshen Boko Haram.
Shugaba Buhari ya kuma jinjinawa dakarun sojin bisa jajircewar su da kuma nasarorin da su ke samu wajen yaki da ‘yan ta’addan, sannan ya ja kunnan dakarun kar su sake ‘yan ta’addan su samu mafaka a fadin Nijeriya.
Haka kuma, Buhari ya bukaci gwamna Buni ya ci gaba da goyon bayan sojojin, tare da cewa rahotannin sirri a tsakanin hukumomi da farar hula za su taimakawa waje kawar da miyagun ayyuka a jihar Yobe da ma kasa baki daya.
A nashi bangaran, Gwamna Buni ya bayyanawa Buhari irin halin tsaro da jihar sa ke ciki, sannan ya mika godiya ga gwamnatin tarayya a kan irin matakin da ta ke dauka na tada hankulan ‘yan ta’addan, tare da cewa matukar dakarun sojin suka cigaba da kokarin da su ke yi, kungiyar Boko Haram ta kusa zama tarihi a Nijeriya.