Home Home Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Sanata Ta Tsige Sanata Jibril Isah Na Mazabar...

Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Sanata Ta Tsige Sanata Jibril Isah Na Mazabar Kogi Ta Gabas

1
0
Wata babbar kotu da ke zama a birnin Awka na Jihar Anambra, ta ci Rundunar ‘yan Sandan Nijeriya tarar Naira miliyan 10 bisa tsare wani dan kasuwa Chukwuemeka Ekwueme ba bisa ka’ida ba.

Kotun sauraron kararrakin zaben Sanata mai wakiltar Kogi ta Gabas ta kori, Sanata Jibrin Isah, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar dattijai mai kula da haraji sakamakon soke zabe a wasu rumfunan zabe 94.

Kotun ta kuma umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC da ta shirya zabe a rumfunan zabe 94 da abin ya shafa.

Shugaban kotun, Justice K.A. Orjiako, wanda ya yanke hukunci kan karar da Victor Adoji, dan takarar jam’iyyar PDP ya gabatar a gabanta, ya amince da bukatar Adoji.

Adoji, ta bakin Lauyan sa, Johnson Usman (SAN), ya kalubalanci dawowar Jibrin Isah kan hujjar cewa an soke zabe a wasu rumfunan zabe inda katin zabe da aka karba ya zarce tazarar kuri’un da aka ayyana nasarar da ya samu.

Mai shigar da kara ya roki kotun da ta soke zaben Isah tare da bayar da umarnin sake gudanar da zabe a rumfunan zabe 94 da abin ya shafa a mazabar majalisar dattawa.