Kotun Koli ta yi watsi da karar da aka shigar, wadda ta nemi tilasta wa Jam’iyyar PDP ta tsai da dan takarar shugaban kasa a daga yankin Kudu maso Gabashin Nijeriya.
Mai Shari’a Adamu Jauro da ya jagoranci zaman kotun ne ya yi wasti da karar, bisa hujjar cewa kotun ba za ta iya sauraren ta ba.
Daya daga cikin wadanda su ka yi zawarcin takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP kuma tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Abia Cosmos Ndukwe ne ya maka jam’iyyar kotu.
A karar da ya shigar, Ndukwe ya nemi kotun ta ba jam’iyyar umarnin ta fito da dan takarar ta na shugaban kasa daga yankin Kudu maso Gabas, amma Mai Shari’a Jauro ya ce mai karar ba ya da hujja, saboda batun tsaida dan takara lamarin cikin gida ne da ya kebanci jam’iyyun siyasa.