Home Labarai Kotun Jigawa Ta Yanke Wa Masu Fyade 4 Hukuncin Daurin Rai Da...

Kotun Jigawa Ta Yanke Wa Masu Fyade 4 Hukuncin Daurin Rai Da Rai

83
0

Babbar Kotun jihar Jigawa da ke zama a Birnin Kudu, ta yanke ma wasu mutane hudu da ta samu da laifin aikata fyade ga kananan yara hukuncin daurin rai da rai.

Wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da wani Umar Danladi da Abdussalam Sale da Auwalu Yunusa da kuma Mu’azu Abdurrahman, bayan ta tabbatar da zarge-zargen da aka yi masu.

An dai yanke masu hukuncin ne daidai da tanadin sashe na 283 na kundin Penal Code na jihar Jigawa na shekara ta 2012 da aka yi wa kwaskwarima.

Da yake yanke hukuncin, Mai Shari’a Musa Ubale ya ce kotun ta gamsu da shaidu da hujjojin da lauyan mai shigar da kara Yahaya Abdullahi ya gabatar wa kotun, ya na mai cewa kotun ta yanke masu hukuncin ne daidai da tanadin dokokin jihar.