Home Labaru Kotun Ƙolin Nijeriya Ta Tabbatar Da Zaɓen Gwamna Adeleke Na Jihar Osun

Kotun Ƙolin Nijeriya Ta Tabbatar Da Zaɓen Gwamna Adeleke Na Jihar Osun

92
0

Kotun Ƙoli ta tabbatar da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ya
tabbatar da zaɓen Sanata Ademola Adeleke a matsayin
gwamnan jihar Osun.

Mai shari’a Emmanuel Akomaye Agim ya karanto hukuncin, bayan rukunin alƙalan kotun biyar sun saurari a ƙarar da tsohon gwamnan jihar Osun Gboyega Oyetola ya ɗaukaka.

Daukacin alƙalan ne su ka amince da matakin korar shari’ar da Gboyega Oyetola ya ɗaukaka, bayan Kotun Ɗaukaka Ƙara ta rushe hukuncin kotun farko da ta ba Gboyega nasara.

Magoya bayan Gwamna Ademola Adeleke da su ka halarci zaman yanke hukuncin dai sun kaure da sowa su na rera waƙoƙin jin dadi.

Idan dai ba a manta ba, a shari’ar da ta gabata wata kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar ta yanke.

Leave a Reply