Kotun daukaka kara dake zama a Abuja ta ba da belin tsohon mai bada shawara a kan harkokin tsaro na kasa, Sambo Daski akan kudi Naira miliyan 100.
Kotun ta kuma umurci Sambo Dasuki, ya kawo mutanen da za su tsaya mashi suma a kan kudi Naira miliyan 100 kowannen su.
Sambo Dasuki na a tsare tun shekarar 2015, kan zargin sama da fadi da wasu kudi da aka ware domin sayan makamai a gwamanatin tsohon shugaban kasa Gudluck Jonathan.
A takardar hukuncin kotun, ta ce duk wadanda za su tsaya wa Dasukin, sai sun kawo wa kotun shaidar cewa suna da kadarori a babban birnin tarayya da kudin su ya kai Naira miliyan 100.
Sambo Dasuki, dai ya musanta zargin da ake masa kan rub da ciki a kan kudaden al’umma.