Home Home Kotu Ta Maida Muhuyi Kan Kujerar Sa Ta Shugaban Hukumar Yaki Da...

Kotu Ta Maida Muhuyi Kan Kujerar Sa Ta Shugaban Hukumar Yaki Da Rashawa Ta Kano

350
0

Kotun Masana’antu ta kasa da ke jihar Kano, ta bada umarnin a maida Muhuyi Magaji Rimingado a matsayin shugaban Hukumar Yaki da Rashawa ta jihar Kano ba tare da bata lokaci ba.

Gwamnatin jihar Kano da majalisar dokoki ta jihar ne su ka shigar da karar Muhuyi, inda su ka nemi kotun ta sauke shi daga matsayin sa.

Da ya ke yanke hukunci, Mai Shari’a Ebeye David Eseimo ya ce ba a yi ma wanda ake karar adalci a karar ba, kuma majalisar jihar ba ta da hurumin korar shi daga matsayin.

Alkalin kotun, ya ce an sallami Muhuyi daga mukamin sa ta hanyar da ba ta dace ba, don haka kotun ta bada umarnin a maida da shi kan mukamin sa ba tare da bata lokaci ba.

Leave a Reply