Home Labaru Kotu Ta Kori Ƙarar Da EFCC Ta Shigar Kan Okorocha

Kotu Ta Kori Ƙarar Da EFCC Ta Shigar Kan Okorocha

117
0

Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta yi watsi da ƙarar da
hukumar EFCC ta shigar a kan tuhumar tsohon gwamnan
jihar Imo Sanata Rochas Okorocha bisa zargin aikata
laifuffukan da su ka shafi almundahanar kuɗi.

Hukumar EFCC dai ta na tuhumar tsohon gwamnan ne da aikata zambar kuɗi da kuma amfani da ofishin sa ta hanyar da ba ta dace ba.

Sai dai kotun ta bayyana tuhumar da cewa tozarta tsarin shari’a ne.

Alƙalin kotun Mai Shari’a Yusuf Halilu, ya ce hukumar EFCC ta shigar da makamanciyar tuhuma a kan tsohon gwamnan a babbar kotun taraya, wadda a cikin watan Disamban da ya gabata ta yanke hukuncin da ya wanke shi.

Leave a Reply