Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kotu Ta Jingine Hukuncin Da Ya Tsige Sufeta Janar Na Yan Sanda, Usman Baba

Babbar Kotun tarayya da ke birnin Awka na jihar Anambra, ta
jingine hukuncin tsige Usman Alkali Baba daga matsayin
shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya.

Rahotanni sun ce yayin yanke hukuncin, Alkalin Kotun mai shari’a Fatun Riman, ya umarci Alkali Baba ya daina ayyana kan sa a matsayin shugaban ‘yan sandan Nijeriya.

Mai shari’a Riman dai ya yanke hukuncin cewa, zaman Baba a kan kujerar shugaban ‘yan sanda bayan ya cika shekarun ritaya ya saɓa wa doka da kundin tsarin mulkin Nijeriya.

Kotun dai ta ɗauki matsayar ne a wata ƙara da Okechukwu Nwafor ya shigar gaban ta.

Da ya ke kalubalantar hukuncin a gaban Kotun, lauyan Alkali Baba ya shaida wa Alkalin cewa ba a yi masa adalci ba a sauraren ƙarar, saboda mai ƙara ya gaza kai ma shi takardar sammaci ta asali.

Exit mobile version