Home Home KOTU Ta Haramta Wa EFCC Bincikar Bello Matawalle Da Jami’an Gwamnatin Zamfara

KOTU Ta Haramta Wa EFCC Bincikar Bello Matawalle Da Jami’an Gwamnatin Zamfara

86
0
Zargin Boye Biliyoyi Nairori A Abuja: Matawalle Ya Rubuta Wasika Ga EFCC

Babbar Kotun Tarayya da ke Gusau a ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a A. B. Aliyu, ta haramta wa hukumar EFCC gayyata ko kuma tsare tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle.

Mai shari’a A.B Aliyu, ya yanke hukuncin ne, biyo bayan ƙarar da Farfesa Mike Ozekhome ya shigar a madadin Gwamnatin Zamfara, inda ya ke ƙalubalantar hukumar EFCC game da gayyata ko tsarewa ko kuma binciken jami’an gwamnatin jihar dangane da yadda aka tafiyar da kuɗaɗen da Majalisar Dokokin Jihar ta kasafta.

Farfesa Mike Ozekhome, ya ce Majalisar Dokoki ta Jihar da Babban Jami’in Bincike na Jihar kaɗai ne doka ta ba hurumin shigar da kara.

Da ya ke yanke hukuncin, Alƙalin ya ce EFCC ba ta da hurumin yin bincike a kan yadda aka raba kuɗaɗen Jihar Zamfara, kuma ba ta da damar gayyatar jami’an Gwamnatin game da yadda aka tafiyar da kuɗaɗen da Majalisar Dokoki ta Jihar ta raba. Kotun ta ce, binciken da EFCC ke ƙoƙarin gudanarwa, wanda har ta kai ga miƙa wasiƙar gayyata ga jami’an Gwamnatin Jihar Zamfara don su je su amsa tambayoyi a kan yadda aka kashe kuɗin shigar jihar ko kuɗaɗen gwamnatin jihar, yunƙurin shiga hurumin da ba nata ba ne ta yi.

Leave a Reply