Home Labarai Kotu Ta Hana Tsige Damagun A Matsayin Shugaban Riƙo Na Jam’iyyar PDP

Kotu Ta Hana Tsige Damagun A Matsayin Shugaban Riƙo Na Jam’iyyar PDP

35
0
Amb. Umar Damagum
Amb. Umar Damagum

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da kwamitin amintattu BOT da majalisar ƙolinta daga cire Umar Damagun a matsayin shugaban riƙo na jam’iyyar.

Mai shari’a Peter Lifu ne ya bayar da umarnin a hukuncin da ya yanke, inda ya ce Damagun ne zai cigaba da zama shugaban jam’iyyar na riƙo har zuwa ranar da za a gudanar da babban taron jam’iyyar a watan Disamban 2025.

Alƙalin ya ce bisa la’akari da sashe na 42 da 47 da 67 na jam’iyyar, a babban taron jam’iyyar ne kawai za a iya zaɓan wani sabon shugaba, inda ya ce dole duk wani ɗan jam’iyyar ya yi biyayya ga kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Mai shari’a Lifu ya ƙara da cewa yanzu zangon shugabancin PDP na Arewa ne, inda ya ƙara da cewa tunda an zaɓi Damagun ne domin ƙarasa zangon mulkin Iyorchia Ayu wanda shi ma ɗan yankin ne, dole ya ƙarasa zangon.

Leave a Reply