Home Labaru Kotu Ta Hana EFCC Kwace Kadarorin Yari

Kotu Ta Hana EFCC Kwace Kadarorin Yari

377
0
Kotu Ta Hana Efcc Kwace Kadarorin Yari
Kotu Ta Hana Efcc Kwace Kadarorin Yari

Babbar kotun tarayya dake Abuja, ta gargadi hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC da Antoni Janar na tarayya da su bi umurnin kotu kan yunkurin kwace kadarorin tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari.

Mai shari’a Maha, ya bukaci hakan a hukuncin da ya yanke na shigar da kara da ya yi na neman hana a kwace masa kadarori, alkalin ya kuma dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 5 ga watan Satumba mai zuwa.

Lauyan dake kare Yari, ya bukaci kotun ta dakatar da hukumar EFCC da Antoni Janar na tarayya daga yin katsalandan a harkokinsa tare da hanashi walwala kamar yadda sashe na 34, 35, 37, 41 da 43 ya tanada a kundin tsarin mulki.

A ranar 26 ga watan Augustan nan ne alkalin ya gayyaci hukumar EFCC da Antoni Janar na tarayya da su bayyana a gaban kotun bisa yunkurin da suka yi na kwace kadarorin Yari.

Leave a Reply