Home Home Kotu Ta Ci Tarar ‘Yan Sanda N10m Kan Tsare Dan Kasuwa A...

Kotu Ta Ci Tarar ‘Yan Sanda N10m Kan Tsare Dan Kasuwa A Anambra

108
0
Wata babbar kotu da ke zama a birnin Awka na Jihar Anambra, ta ci Rundunar ‘yan Sandan Nijeriya tarar Naira miliyan 10 bisa tsare wani dan kasuwa Chukwuemeka Ekwueme ba bisa ka’ida ba.

Wata babbar kotu da ke zama a birnin Awka na Jihar Anambra, ta ci Rundunar ‘yan Sandan Nijeriya tarar Naira miliyan 10 bisa tsare wani dan kasuwa Chukwuemeka Ekwueme ba bisa ka’ida ba.

Tarar dai, ta shafi Mataimakin shugaban ‘yan sandan Nijeriya Abutu Yaro, wanda shi ne mai kula da harkokin ‘yan sanda a shiyya ta 13.

Da ya ke yanke hukuncin, Mai Shari’a D.A. Onyefulu, ya kuma bukaci ‘yan sandan su biya mai karar Naira dubu 200 a matsayin kudin shari’a.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito Alkalin ya ba da umarnin kada ‘yan sanda su yi wa Ekwueme wata barazana ko tsare shi a kan batun da ya yanke hukunci.

Hukuncin dai ya biyo bayan karar da Ekwueme ya shigar a kotun, inda ya nemi kotu ta kwato masa ‘yancin sa a wajen ‘yan sanda.

Leave a Reply