Home Home KOTU Ta Ci Tarar Tsohon Ministan Buhari, Saboda Ya Yi Wa Atiku...

KOTU Ta Ci Tarar Tsohon Ministan Buhari, Saboda Ya Yi Wa Atiku Sharri, Ƙage Da Yarfe

91
0
Kotun ƙoli da ke birnin London, ta ce ‘yan Nijeriyar da ke son shigar da ƙarar kamfanin man fetur na Birtaniya Shell sun makara.

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta kori ƙarar da tsohon Ƙaramin Ministan Ƙwadago Festus Keyamo ya shigar a kan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar.

Festus Keyamo dai ya maka Atiku Atiku kotu, inda ya nemi kotu ta umarci hukumaer EFCC da sauran hukumomin yaƙi da cin hanci su kama shi bisa zargin rashawar da ake yi masa.

Da ya ke yanke hukunci, Mai Shari’a James Omotosho ya kori ƙarar tare da kiran ta a matsayin shirme da shiriritar sharri, don haka kotun ta ci Festus Keyamo tarar naira miliyan 10 a matsayin diyyar bata suna.

Kotun, ta umarci Keyamo ya biya Atiku Abubakar diyyar ɓata masa lokaci Naira miliyan 5, Sannan ya biya hukumar ICPC diyyar ɓata masu lokaci da ya yi.

Haka kuma, kotun ta umarci Keyamo ya riƙa ɗora masu ƙarin kashi 10 duk shekara idan ya ƙi biyan diyyar a cikin shekara ɗaya.

Leave a Reply